Wednesday 21 January 2026 - 00:02
Mai girma Jagoran Juyin Juya Hali Mai Girma Yana da Tsarin Wayewa ta Alƙur'ani / Miliyoyin Mutane sun Tsaya har Zuwa Digon jininsu na ƙarshe don kare Jagora

Shugaban Makarantun ilimin Addinin Musulunci (Hauza) ya bayyana cewa: "Jagoran Mu Mai Girma suna da sojoji masu jihadi da sadaukarwa da yawa a duk faɗin duniya, kuma duk wani barazana ko tauye martabarsa ba zai taɓa zama karbabben abu ga al'ummar Musulunci ba kuma miloyin mutane sun tsaya har zuwa digon jini na ƙarshe don kare wannan tsattsarkan tunaninsa da kuma shi kansa."

A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, Ayatullah Alireza A'arafi, shugaban makarantun Hauza, a taron rufe bikin Alqur'ani da Hadisi na Jami'ar Al-Mustafa (SAWA) karo na 31 da kuma babban bikin girmamawa da bayyana halayen Alkur'ani na Babban Jagoran Musulunci, wanda aka gudanar a yau a babban dakin taro na Quds na Cibiyar Ilimi ta Imam Khomeini (RA) a birnin Qom, ya ce: "A fagen Alkur'ani Mai Girma, abin takaici, mun ga yawaitar wuce gona da iri a cikin tarihin Musulunci, kuma wannan littafin na Allah Mai Shiriya ya ragu a rayuwar ɗaiɗaikun mutane da kuma zamantakewar al'ummar Musulunci."

Memba na manyan malaman shari'a na majalisar kwararru ya kara da cewa: "A gefe guda, an gabatar da akidar 'Littafin Allah ya ishe mu' (Hasbuna Kitabullah) a gaban 'Itra' (Iyalan Annabi), kuma aka gabatar da Alkur'ani ba tare da mai bayyani ba. Wannan kuskuren akidar ya haifar da rudani da yawa a fagen tunani da aiki. Don haka, tabbas 'Hasbuna Kitabullah' babban karkata ne da ra'ayi mara kyau."

Shugaban makarantun ilimin addinin Musulunci ya ci gaba da cewa: "A gefe guda kuma, wasu sun gabatar da ra'ayin ware Alkur'ani, inda suka ayyana hadisi a matsayin kadai tushen tsarin Musulunci, kuma misali bayyananne na hakan shi ne masu bin hadisi (Akhbariyun). Wadannan ra'ayoyin biyu na kuskure ne suke sa mu shiga cikin rudani da ɓata."

Shugaban makarantun Hauza, yana mai nuni ga halayen Alkur'ani na Babban Jagora, ya ce: "Babban Jagoran mu tun yana matashi ya kulla zumunta da Alkur'ani Mai Girma. Wannan zumunta ta kasance ta aiki da aiki kuma ta tunani da akida. Zumunta da Alkur'ani a lokacin samartaka ana yawan ba da shawarar sa, kuma darajar ɗaliban Hauza a yau ita ce, tun daga farko su kasance a tare da Alkur'ani."

Ayatullah A'arafi ya bayyana cewa: "Zumunta da sha'awar Alkur'ani Mai Girma gaskiya ce da kowane matashi ko ɗalibi a makarantar ilimin addinin Musulunci da dalibai a jami'o'i ke bukata. Babban Jagoran Musulunci tun daga wancan lokacin na matasa suna da wannan zumunta da Alkur'ani Mai Girma, kuma a yau suna ba da shawarar ta."

Memba na manyan malaman shari'a na majalisar kwararrun ya lurar cewa: "Babban Jagoran Musulunci a fagen tafsiri, sun bi hanya mai daidaito. Masu tafsiri wani lokaci suna shagaltuwa da kalmomi da yare da zurfin nazarin adabi, sukan tsaya cikin wannan tekun. A gefe guma kuma, muna da mutanen da ke da ra'ayi mai rai da kyau game da Alkur'ani amma tushensu ba su da ƙarfi. Tunanin Babban Jagora ya dogara ne akan zurfin nazarin kalmomi da tushen ayoyi, kuma yana da wuya a sami makamancinsa a wannan fage."

Jagoran Musulunci Yana da Tsarin Wayewa ta Alƙur'ani Mai Girma

Ayatullah A'arafi ya ci gaba da cewa: "Wasu suna da zurfin nazari game da rarrabe ayoyin Alkur'ani amma ba sa bayar da tafsiri bayyananne. Amma Babban Jagora ya haɗa duka biyun tare. Haka kuma, suna da tsarin wayewa na Alkur'ani Mai Girma."

Memba na kwamitin gudanarwar makarantun ilimin addinin Musulunci ya ce: "Tsarin tunanin ilimin halayyar dan Adam na tarbiyya daga cikin sauran siffofin tafsirin Babban Jagoran Musulunci ne. Tafsirinsa, na ijtihadi ne, ma'ana bai kunshi batutuwa marasa ƙarfi da tushe ba. Tafsirin Jagora cikakke ne, mai rai, kuma na ijtihadi."

Shugaban makarantun Hauzar ya ce: "Imam Khamenei mawallafin tafsiri ne wanda sama da rabin ƙarni koyaushe yana cikin hatsarori daban-daban a fagen aiki. Akwai manyan mutane da suka zauna a lungu suna faɗin maganganu masu kyau, kuma akwai mutanen da suka kasance masu fafutuka a fage mai nauyi. Amma shi, yana da zurfin ilimi, kana kuma ya kasance yana a fage mai nauyi na gwagwarmaya, kuma muna ganin taruwar tunani da aiki a tare da shi."

Trump ya Sani Cewa Juyin Juya Halin Musulunci Ba Shi da Kwatankwaci da Kowace Gwamnati ko Ƙungiya a Duniya

Ayatullah A'arafi, yana mai nuni ga kalaman banza na Trump a kan Jagoran juyin juya halin Musulunci, ya lurar cewa: "Trump ya san cewa juyin juya halin Musulunci ba shi da kwatankwaci da wannan gwamnati ko wancan gwamnati, da wannan ƙungiya ko waccan ƙungiya a duniya. Al'ummar Iran da kuma gudanyar tunanin Musulunci sun sha bamban da gudanya daban-daban wanda Amurka ta shiga rikici da su kuma ta ƙaddamar da ɗaruruwan yaƙe-yaƙe a kansu, ta rushe ƙasashe da yawa."

Miloyin Mutane Sun Tsaya Har Zuwa ga Digon Jininsu na Karshe don Kare Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci

Memba na manyan malaman Majalisar kwararru ya ce: "Wannan kuskuren lissafi ne a kwatanta tunanin juyin juya halin Musulunci da jagora mai daraja da sauran tunanuka na duniya, da farko wannan maganganun banza da karairayin da aka fade su a yan kwanakin nan zasu koma kansu ne. Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci yana da sojojin gwagwarmaya kuma masu sadaukarwa da yawa a ko ina a fadin duniya kuma kowanne irin barazana ga mutuncin jagora ba abin da al'ummar Musulmi zasu yarda da shi ba ne, akwai miliyoyin mutane wadanda suke a tsaye har digon jininsu na karshe don kare wannan tunani mai tsarki da kuma shi kansa jagoran.

A karshe Ayatullah A'arafi ya jaddada: "A yau wannan amon ya bazama a duk fadin duniya da duniyar Musulunci, kuma zamu ci gaba da bin wannan hanya mai haske komai wahala.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha